Wasu Da Dama Sun Jikkata Bayan Gobarar New York Da Ta Kashe Mutane 19

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Da Dama Sun Jikkata Bayan Gobarar New York Da Ta Kashe Mutane 19

Likitoci sun yi famar ceto rayukan mutane da dama da suka samu munanan raunuka a ranar Litinin, lokacin da hayakin wuta ya buge su ko kuma ya makale da su a cikin gidajensu a wani babban bene na birnin New York. Mutane 19 da suka hada da yara 9 ne suka mutu a gobarar.

An kwantar da mutane da dama a asibiti, kuma kusan 13 na cikin mawuyacin hali bayan gobarar da ta tashi a ranar Lahadi a unguwar Bronx, wacce ita ce gobara mafi muni a birnin cikin shekaru talatin.

Masu bincike sun tabbatar da cewa wata na'urar zafafa daki ta lantarki da ke da matsala, wacce aka kunna don ba da ƙarin dumi da sanyin safiya, itace sanadin tashin gobarar a ginin mai hawa 19.

Wutar ta lalata wani ɗan ƙaramin sashe na ginin ne kawai, amma hayaƙin ya shiga ta ƙofar ɗakunan da ke buɗe zuwa matakalan ficewa - wacce itace hanya ɗaya tilo da za'a iya bi a fice don tserewa daga wautar - ya zama cikin duhu mai ban tsoro.

Wasu mutane sun kasa tserewa ne saboda yawan hayakin, in ji kwamishinan Hukumar kashe gobara Daniel Nigro. Wasu kuma sun kasa ne kawai a kokarinsu na ficewa. Ma’aikatan kashe gobara sun sami wadanda abin ya shafa a kan kowane bene, da yawa zuciyarsu ta cije, har sun kasa iya numfashi, in ji Nigro.

Kwamishinan kashe gobara Daniel Nigro ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano yadda gobarar ta tashi da kuma fahimtar ko da akwai matakan da suka kamat ace an dauka don shawo kanta.

-AP