Wasanni A Takaice

  • Murtala Sanyinna
Wasanni

Wasanni

Yanzu haka dai al’amura sun kankama a wani katafaren gidan marayu da shahararren dan wasan Super Eagles ta Najeriya, Odion Ighalo ya gina a birnin Ikko, wanda tuni ya soma da aikin tsugunar da marayu 40.

Gidan marayun wanda aka kiyasta ya lakume kudi kusan naira miliyan 500, an gina shi ne a unguwar Ijegun a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Odion Ighalo

Odion Ighalo

An kuma gina gidan marayun ne a karkashin gidauiniyar tallafawa marasa galihu ta Ighalo, da zimmar tabbatar da mafarkin dan wasan na kyautata rayuwar marayu, kamar yadda ya sha alwashin yi muddin ya sami daukaka a harkar kwallon kafa.

Ana kula da kusan dukkan bukatun rayuwa na marayu a gidan, ciki har da ilimi da kuma horar da su wasanni, har lokacin da suka kai shekaru 18 da haihuwa, kuma ana sa ran ci gaba da kara yawan marayu nan gaba kadan a cibiyar.

Kungiyar kwallon kafar Newcastle United ta Ingila da ke fafata gasar Premier ta kaddamar da zawarcin dan wasan gaba na Najeriya Moses Simon da ke taka leda a kungiyar Nantes ta kasar Faransa.

Simon na daga cikin zaratan 'yan wasan da tauraronsu ya haska sosai a gasar kwallon kafar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala kwanan nan a kasar Kamaru.

Moses Simon

Moses Simon

Rahotanni sun bayyana cewa Simon ne kan gaba a jerin sunayen ‘yan wasan da kungiyar ke farautarsu, kuma tuni ta yi kwakkwaran shirin ganin ta mallaki dan wasan.

Mujallar wasanni ta Own Goal ta ruwaito cewa sayen Simon na iya cin kungiyar ta Newcastle zunzurutun kudi har fam miliyan 20, a yayin da kuma kungiyar ta ke da kudurin ba shi kwantaragin da albashinsa zai kama fam 100,000 a kowane mako.

A Ingila din kuma yanzu haka kungiyoyin Manchester United da Liverpool suna gwabza yakin zawarcin matashin dan wasan Barcelona ta kasar Spain, Ronald Araujo.

Dukan kungiyoyin na Ingila 2 dai sun yi ittifakin cewa samun Araujo, wanda yanzu haka bai sabunta kwantaragin zaman na shi a Barcelona ba, zai karfafa wa ‘yan wasansu.

Ronald Araujo

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an kungiyar ta Barcelona sun jima suna tattaunawa da wakilan dan wasan akan sabon kwantaragi, to amma har yanzu ba su cimma daidaito ba.

Araujo ya koma Barcelona ne daga kungiyar Boston ta kasar Uruguay a shekara ta 2018, akan kwantaragin farko na fan miliyan 1.4 kafin kara wani kwantaragin daga bisani na fam miliyan 2.9.

A gobe Talata za’a soma fafata wasannin zagayen ‘yan 16 na gasar zakarun Turai, inda kungiyar PSG ta kasar Faransa za ta fafata da Real Madrid ta kasar Spain, yayin da ita kuma Manchester City ta Ingila, za ta kece raini da Sporting ta kasar Portugal.

Gasar Zakarun Turai

A ranar jibi Laraba kuma Inter Milan ta kasar Italiya, ta kara da Liverpool ta Ingila, kana kuma Bayern Munich ta kasar Jamus ta fafata da Salzburg ta kasar Austria.