Wanne Mataki Ya Kamata Matasa Da Iyaye Da Gwamnati Su Dauka Dan Kaucewa Bangar Siyasa?

A lokuta da dama 'yan siyasa kan yi amfani da matasa wajan yakin neman zabe, amma bayan sun dare kan ragamar mulki sai su juya masu baya, ta dalilin haka ne a wannan karon muke so mu ji ra'ayoyin ku akan wadanne matakai matasa da kansu, da iyaye da kuma gwamnati ya kamata a dauka domin kaucewa irin wannan lamari da ke kai yawancin matasa ya baro?

Muna bukatar ra’ayoyin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.

Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com