Wanne Irin Kasafin Kudi Yan Najeriya Ke Bukata?

Kasafin Kudin shekara 2016 da Shugaba Mohammadu Buhari ya mika wa Majalisar Dokokin Najeriya a watan Disamba da ta gabata, ya zama kasafin kudin farko da aka yi ta jayayya akan sa. Da farko an yi zargin ya bata, sai kuma aka ce an sauya kasafin kudin, daga baya kuma aka ce iri uku daban daban aka gano a majalisar.

A lokacin da ya gabatar da wannan kasafin kudi wanda shine kasafi na farko da ya kai Naira Tiriliyon 6.8, kuma mafi tsoka a tarihin Najeriya, shugaba Buhari ya bayyana kasafin ne a matsayiin kasafin kudi da ake samar da kudade ga ayyukan da za a yi, ba wai kasafin kudi da za a turawa ma’aikata ta kashe a shekara ba.

Sai gashi kasafin ya fuskanci kalubale da dama a cikin watanni uku, data kasance a majalisar kasa. Baya ga bacewa da akace tayi, a kwai rahotanni da ke cewa an sabantashi har sau uku.

Wanne kasafin ne a cikinsu majalisar tace za ta aiwatar gobe 17 ga wata? Tambayar kenan da wakiliyar Muryar Amurka, Madina Dauda, tayiwa shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Ali Ndume, inda yace kasafin kudin bazai banbanta ba da abinda shugaban kasa ya kai musu, sai wasu yan gyara da akayi domin a tabbatar da adalci.

Wata majiya kwakwkwara ta fadawa Muryar Amurka cewa, ya zuwa karshen wannan wata al’ummar Najeriya zasu tashi cikin walwala da jin dadi, domin zasu sami kasafin kudi da zasuyi alfahari da shi.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wanne Irin Kasafin Kudi Yan Najeriya Ke Bukata? - 3'26"