Ita dai wannna kungiyar na cikin kungiyoyin dake bada tallafi ga al'ummomin da bala'o'i da kuma tashe tashen hankula ke shafa a duniya.
Yayin wata ziyarar data kai jihar Adamawa, jami'ar kungiyar a Najeriya, Malama Sarah Ndikumana, ta ce dole a hada hannu wajen agazawa al'ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya. kuma baya ga jihar Adamawa kungiyar na bada irin wannan tallafi a jihohin Borno da Yobe, da suma ke fama da matsalar Boko Haram.
Tun farko da yake wa tawagar ta IRC maraba, gwamnan jihar Adamawa Bindo Jibrilla, ya yaba ne da irin taimakon da irin wadannan kungiyoyi ke badawa ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.
Kuma wannan ma na zuwa ne yayin da kasar Kamaru ke haramar sake iza keyar yan Najeriya fiye da dubu 56 da yanzu haka ke gudun hijira a Kamaru.
Domin karin bayani.