Shugaba Muhammad Buhari na Najeriya ya yi tur da harin da aka kai ranar Lahadi a Grand Bassam Resort dake kasar Ivory Coast da kakkausan lafazi.
Da yake gaisuwar ta'aziya da nuna alhininsa ga shugaban kasar Alassane Ouattara ta wayar tarho, shugaban Najeriya Buhari ya mika ta'aziyar gwamnatin tarayyar Najeriya tare da al'ummar kasar ga ilahirin mutanen Ivory Coast yayinda suke juyayi da zaman makokin 'yan kasar da jami'an tsaronsu da masu yawon bude ido da suka rasa rayukansu a mummunan harin.
Shugaban Najeriya ya jaddada wa takwaransa cikakken goyon bayan Najeriya a wannan lokacin da kasar ke cikin wani mugun hali da tunanin yadda zata fuskanci sakamakon mugun hari da kuma yadda zata shawo kan sabon kalubalen tsaro da ta'addancin ya haddasa.
Shugaba Buhari yace yanzu fa ta'adanci bashi da iyaka, yana ketarawa ne daga kasa zuwa kasa. Shugaba Buhari ya sake nanata kiran da ya yi da cewa lokaci ya yi da kasashen duniya zasu hada karfi da karfe su yaki 'yan ta'ada da masu goyon bayansu.
Yace a Mali sun kai hari otel inda suka kashe mutane 21. Sun kashe fiye da mutane 130 a hare-haren da suka kai Paris babban birnin Faransa. Haka ma a Burkina Faso sun kashe mutane 28.
Yace "ta'adanci bai san iyakokin kasashe ba. Dalili ke nan da yakamata kasashen duniya su hada kawunansu, su dauki matsayi daya kan yadda zasu murkushe wadanda suka mayar da ta'adanci sana'a ko kasuwanci", inji Shugaba Buhari.
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya godewa shugaban Najeriya Buhari da gaisuwar ta'aziya da goyon bayan kasar.