A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin garin Erana mai iyaka da yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya yi karin bayani ta wayar salula inda ya bayyana cewa, ‘Sun zo ne suka dinga banka wa gidaje wuta tare da dasa bama-bamai a cikin gari, akwai motar civil defense daya ma da ya taka bam din har ya tarwatsa motar.”
Duk da ya ke kokarin jin tabakin jami’an na civil defence a jihar Nejan yaci tura , sai dai rundunar yansanda na jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin.
A bayaninsa, Monday Bala Kuryas kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, ya ce yanzu haka 'yan sanda masu aiki da bama-bamai za su je su ga yadda za su cire sauran bama-baman.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga gwamnatin jihar Neja.
Wannan hari na bom dai tamkar wata alama ce dake nuna cewa mayakan boko haram sun mamaye madatsar ruwan na shiroro daya daga cikin tashoshi 3 dake samar da hasken lantarki a Nigeria.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5