Wani sabon kumbo zai yi tattakin da babu wani kumbon da ya taba yin irinsa a baya zuwa ga ranar bil Adama.
Wannan kumbon bincike na Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka mai suna Parker Solar Probe zai kusanci rana ta yadda zai kasance a wani falaki mai nisan mil miliyan 4 daga doron ranar. Kumbon da ya fi kusantar rana a can baya, yayi shawagi ne a wani falaki mai nisan mil miliyan 28 daga kan doron ranar.
An kera wannan sabon kumbo ta yadda zai iya jure tsananin zafi na rana fiye da kowane kumbo a can baya. Za a nade kumbon da wata irin garkuwar zafi ta zamani wadda zai iya jure zafi mai tsananin awu dubu 2 da 500 a ma’aunin zafi na Fahrenheit.
Kafin kumbon ya iya kaiwa ga wannan falaki a kusa da doron ranar, zai yi ta shawagi yana wuce duniyar Venus, ko tauraruwar nan da ake kira Zara, wadda zata kara ingiza shi har sau bakwai a cikin shekaru bakwai dake tafe.
An shirya harba wannan kumbo ranar Asabar kafin ketowar alfijir.
Your browser doesn’t support HTML5