Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Shafukan Yanar Gizo Facebook, Twitter, Da Google Zasu Fuskanci Doka


A watan gobe ne ake sa ran shugabanin kamfanonin Facebook, Twitter da Google, zasu gurfana gaban majalisar Amurka, don bayyana ma ‘yan majalisun kokarin da su keyi wajen magance satar bayanai a shafufukan yanar gizo.

A jiya ne shugaban kwamitin binciken asiri na majalisar Sanata Richard Burr, ya bayyana hakan wanda yake cewar zasu duba yadda kasar Rasha da ma wasu kasashe suke juya akalar shafukan yanar gizo a fadin duniya.

Sai ya kara da cewar babban burin wannan taron na ganawa da manyan kamfanonin shafin yanar gizo, da za’ayi a ranar 5 ga watan Satumba shine, “Don muji wadannen irin shirye shirye su keyi, da kuma kara matsa masu lamba don daukar kwararan matakai da suka dace wajen magance matsalar satar bayanai”

Haka kuma zamu yi aiki hannu da hannu da kamfanonin don ganin an magance duk wata matsala da akan yada ta kafofin sadarwar yanar gizo, a cewar shugaban binciken Mr. Richard.

Domin kuwa kamfanonin zasu iya yin hobbasa wajen kare demokaradiyya a fadin duniya, ya kuma kara da cewar, duk kuwa da kwashe watannin 18 da mukayi muna binciken wannan matsalar, akwai tabbatacin cewar irin illlar da kasar Rasha tayi ma demokaradiyar kasar nan ya wuce haka.

Ranar Talata ne kamfanin facebook ya sanar da kulle wasu shafuka na mutane 32, da ake amfani da su wajen cin zarafin wasu ‘yan siyasar kasar Amurka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG