Wani mutum da aka yi wa allurar rigakafin cutar ta Covid-19 har sau 10 a rana guda a madadin wasu mutane, ya sa hukumomi sun kaddamar da bincike kan lamarin.
Astrid Koornneef, manajan kungiyar ayyuka na rigakafin Covid-19 da shirin rigakafi na New Zealand, ta ce Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta san da lamarin kuma tana daukansa da muhimmanci kamar yadda jaridar New York Post ta ruwaito.
Ma'aikatar ta ki ta bayyana inda lamarin ya faru a kasar ta New Zealand.
Kwararriya a fannin ilimin allurar rigakafi, Farfesa Helen Petousis-Harris ta kira shi "mai son kai " da cin gajiyar wani da ke buƙatar kuɗi.
Yana iya haifar da mummunar illa daga mutanen da ba a yi musu allurar ba, saboda za su iya ci gaba da yada kwayar cutar, a cewar ta.
"Mun san cewa akan yi kuskure a ba mutane har allurai biyar a cikin kwalba maimakon a gauraya shi, mun san hakan ya faru a kasashen waje, kuma mun san da wasu kurakuran alluran sun faru kuma ba a sami matsala na dogon lokaci ba." Ta kara da cewa.
Amma Farfesa Petousis-Harris ta ce karbar allurai da yawa na rigakafin Covid-19 bai dace ba, tana mai cewa idan aka ba mutane allurai masu yawa, suna samun karin zazzabi, ciwon jiki da ciwon kai.
Ana zargin mutumin, wanda aka fahimci ya ziyarci cibiyoyin rigakafin da dama, cewa an biya kudi don karban allurer ne, a cewar Stuff.
A cewar Koornneef ta ce mutanen da suka sami ƙarin alluran rigakafi fiye da shawarar da aka ba su ya kamata su nemi shawarar asibiti da zaran nan da nan.
"Karbar allura da sunan wani na da haɗari. Wannan na jefa mutune cikin haɗari saboda za’a zatan mutum ya karbi allura, alhalin bai yi.
Bugu da kari, Ms Koornneef ta ce, idan mutum zai yi allurar rigakafin kamuwa da cuta a karkashin abin da aka zaci tantance bayanan lafiyar kansa ba zai nuna cewa an yi masa allurar ba. Wannan zai iya shafar yadda ake kula da lafiyarsu a nan gaba.