Wani Mutum Ya Koma Gida Bayan Shafe Shekaru 38 A Kurkuku

An tsare dimbin bakin haure, ciki har da Suhail Harmawi daga kasar Lebanon wanda ya koma kasarsa a jiya Litinin bayan ya shafe shekaru 33 a garkame.

Wani mutun na asalin Jordan ya koma kasarsa bayan shafe shekaru 38 a kurkukun Syria, a cewar wani jami’i a yau Talata, rushewar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta kawo karshen kunchin jiran da iyalansa suka kasance a ciki.

An tsinci mutumin, mai suna Osama Bashir Hassan al-Bataynah, a Syria ya fita hayyacinsa kuma yana fama da matsalar mantuwa”, kamar yadda jami’in ma’aikatar wajen Jordan Soufian al-Kodat ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

A cewar Kodat dangin mutumin sun kai rahoton batansa a 1986 lokacin yana da shekaru 18 da haihuwa, kuma tun lokacin yake daure a kurkuku.

Kungiyoyin fafutukar farar hula sun zargi Assad daya jagoranci gwamnatin kama karya da kamen jama’a babu dalili da azabtarwa dama kisa a gidajen yari.

An tsare dimbin bakin haure, ciki har da Suhail Harmawi daga kasar Lebanon wanda ya koma kasarsa a jiya Litinin bayan ya shafe shekaru 33 a garkame.