Wani Mutum Ya Harbe Makwabtansa Biyar Har Lahira A Amurka

Unguwar da harbin ya faru, a jihar Texas

Mutumin wanda aka bayyana sunansa a matsayin Francisco Oropeza mai shekaru 38 ya tsere bayan da ya harbe mutanen a garin Cleveland mai tazarar kilomita 72 daga Houston babban birnin jihar ta Texas.

Wani mutum a jihar Texas da ke Amurka, ya harbe makwabtansa biyar har lahira, ciki har da yaro dan shekara takwas.

Mutumin ya dauki wannan mataki ne bayan da makwabtan nasa suka nemi da ya daina harba bindiga a farfajiyar da ke bayan gidansa saboda suna so su yi bacci a cewar hukumomi.

Mutumin wanda aka bayyana sunansa a matsayin Francisco Oropeza mai shekaru 38 ya tsere bayan da ya harbe mutanen a garin Cleveland mai tazarar kilomita 72 daga Houston babban birnin jihar ta Texas.

Wasu daga cikin mazauna unguwar da lamarin ya faru, sun ce ba bakon abu ba ne ka ji mutane suna harba bindiga musamman a karshen mako, wata al’ada da ake ganin suna yi ne don huce gajiyar aiki da suka sha a cikin mako.

Shugaban ‘yan sandan yankin San Jacinto da lamarin ya faru, Greg Capers, ya ce Oropeza ya yi amfani da bindiga kirar AR kuma yayin da ake ci gaba da nemansa har zuwa yammacin Asabar, hukumomi sun yi gargadin cewa a yi hattara da shi domin mai yiwuwa har yanzu yana dauke da makami.

Capers ya ce, shekarun mutanen da suka mutu sun kama tsakanin 8 zuwa 31 kuma dukkansu ‘yan asalin kasar Honduras ne.