Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mace Ta Kashe Mutane 7 A Wata Makaranta


Jami'an Tsaro suna fitar da yara a wata makaranta, Nashville, Tennessee inda aka kai hari
Jami'an Tsaro suna fitar da yara a wata makaranta, Nashville, Tennessee inda aka kai hari

Yau Litinin wata mace ‘yar bindiga ta kashe yara 3 da manyan mutane 4, a makarantar Christian grade a jihar Tennessee da ke kudancin Amurka, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

To sai dai ‘yan sanda sun harbe tare tare da kashe maccen nan take, wadda da farko aka bayyana cewa ‘yar matashiya ce. Daga bisani hukumomi sun tabbatar da cewa wadda ake zargin ‘yar shekaru 28 da haihuwa ce.

Kakakin hukumar ‘yan sandan birnin Nashville, Don Aaron, ya ce ‘yar bindigar tana rike ne da akalla bindigogi masu sarrafa kan su guda 2, da kuma karamar bindiga daya.

Yara suna gudu daga makarantar da aka kai hari a Nashville
Yara suna gudu daga makarantar da aka kai hari a Nashville

Ya ce ‘yan sanda sun soma samun kiran gaggawa ne da karfe 10:13 na safe dangane da ‘yar bindigar a makarantar Covenant, wata makarantar mai zaman kan ta a Nasville.

Aaron ya ce jami’an ‘yan sandan da suka isa wurin sun ji karar harbin bindiga yana fitowa daga hawa na 2 na ginin makarantar.

Ya ce jami’ai 2 daga cikin ayarin ‘yan sanda 5 da suka kai dauki wajen ne suka harbe ta a harabar makarantar, kana kuma ta mutu da karfe 10:27 na safe.

XS
SM
MD
LG