Sadisu Salisu, matashi mai wakilta kungiyar Mafarka Youth Development Initiative, kuma mai aiki da wata kungiya da ke kula da almajirai, da kuma marayu musamman wadanda rikicin Arewa maso Gabashin Najeriya ya shafa.
Ya ce matsalolin bara da almajiranci su yi tsanani yanzu, amma mutane da dama ne ke jahiltar al’amarin, inda ake tunanin duk mai bara almajiri ne, alhalin ba haka abin ya ke ba, domin addinin Muslunci ma bai yarda da bara ba.
Sadisu ya ce al'amari na bara abu ne mai cin rai da takaici, ganin ana alakanta almajiranci da Musulunci, saboda haka ya zama wajibi matasa su ja hankalin gwamnati domin tabbatar da an shawo kan wannan matsalar.
"Akwai bambanci tsakanin almajiranci da kuma barar da ake yi a yanzu, domin kuwa, a cewar Sadisu, da shi almajiri ne har taba yin bara a wancan lokacin.
Ya kara da cewa gwamnati za ta iya canza wannan matsalar ta hanyar fito da wasu hanyoyi da zasu dakile bara ta hanyar budewa almajiran tsangayu da zasu kasance karkashin kulawarta.
Ya ce daga cikin hanyoyin da za’a iya amfani wajen magance almajirai da suke bara, da wadanda suke karatun Alkur’ani, sun hada da tsara manhajar ilimi, tare da tattaunawa da wadanda suke harkar karatun almajirianci, da kuma sanya doka idan bukatar hakan ta taso.
A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5