Masu bincike na Amurka sun ce wani sabon maganin yaki da cutar Ebola da aka yi gwajinsa a kan wasu birrai da suka kamu da cutar, ya nuna alamun zai yi aiki sosai.
Masana kimiyya daga wata cibiyar yaki da cuce-cuce masu yaduwa ta rundunar sojojin Amurka, sun ce maganin ya kare kashi sittin daga cikin 100 na birrai daga wannan cuta.
Irin wannan maganin da aka yi gwajinsa a kan birran, ya kuma kare dukkansu daga kwayar cutar Marburg, wadda ita ma kamar kwayar cutar Ebola, tana cikin wani jinsin kwayoyin cuta da ake kira "Filoviruses."
Masu binciken suka ce Hukumar Kula da Lafiyar Abinci da Magunguna ta Amurka, ta bayar da iznin a yi gwajin wannan maganin a kan mutane.
Wannan maganin yana aiki ne ta hanyar hana kwayar cutar haihuwa a cikin jiki, har sai kwayoyin halitta masu kare jiki daga cuta sun samu sukunin yadda zasu yaki kwayar cutar.
An buga sakamakon wannan bincike nasu a cikin mujallar nan ta "Nature Medicine."
Wasu daga cikin jinsunan kwayar cutar Ebola, su na kashe kashi 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da su. Cutar tana yaduwa ta hanyar taba duk wani abu mai ruwa-ruwa da ya fito daga jikin wanda yake dauke da wannan cuta.
Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce tun lokacin da aka fara gano cutar Ebola a shekarar 1976, cutar ta kama mutane fiye da dubu 1 da 800, ta kuma kashe dubu 1 da 200 daga cikinsu.