Jami’an kasar Pakistan sunce hare haren bama bamai guda biyu dabam dabam da aka kai yau litinin sun kashe akalla mutane talatin da uku. Hukumomi sun fada cewa wani mai harin kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin Masalaci a yankin kudancin Waziristan ya kashe wani Malami mai suna Maulana Noor Mohammed da akalla mutane ashirin da biyar. Hukumomi sunce Malami ne aka auna a wannan hari a wannan yanki da aka dauka babar tungar kungiyar Taliban. A wani wuri dabam kuma, wani bam ya tashi a wajen wani taron shugabanin kabilu a lardin Kurram, ya kashe mutane bakwai. Babu dai wata kungiyar data bugi kirji, ta yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai wannan hari. A baya dai yan yakin sa kan Islama su kan kai irin wadannan hare hare, to amma kuma sun dan sausauto tun lokacinda kasar Pakistan ta fara fama da matsalar ambaliyar ruwa.
Jami’an kasar Pakistan sunce hare haren bama bamai guda biyu dabam dabam da aka kai yau litinin sun kashe akalla mutane talatin da uku.