Jami'an Najeriya sun ce yawan mutanen da suka mutu a sanadin annobar cutar kwalara a arewacin kasar ya karu zuwa 231, yayin da mutane fiye da dubu 4 da 600 suka kamu da wannan cuta.
Babban jami'in kula da yaduwar cuce-cuce a ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayyar Najeriya, Henry Akpan, shi ne ya tabbatar da wannan adadi ga 'yan jarida a birnin Abuja.
Da alamun jihohin da wannan cuta ta fi yin illa su en Bauchi da Borno. Mutanen da cutar ta kashe a wadannan jihohi biyu kawai ya haura dari daya.
Jami'ai su na dora laifin wannan annobar a kan gurbataccen ruwan sha da kuma da kuma rashin tsabta. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ambaci Akpan yana fadin cewa ma'aikatarsa ta kafa cibiyoyin tallafawa mutanen da suka kamu da cutar tare da dakile yaduwarta.
Kwalara tana haddasa amai da gudawa, abinda ke sa ruwa ya kare a jikin mai fama da ita.