Wani Likita Dan Asalin Kasar Congo Ya Sami Lambar Yabo Saboda Jinyar Matan Da Aka Yi Wa Fyade

  • Ibrahim Garba

Wasu matan kasar Congo kenan ake masu jawabi game da matsalar fyade.

Wani likitan Janhuriyar Demokaradiyyar Congo ya sami lambar yabo daga wata gidauniyar kasar Belgium saboda ya taimaka wa matan da aka yi masu fade.

Wani likitan Janhuriyar Demokaradiyyar Congo ya sami lambar yabo daga wata gidauniyar kasar Belgium saboda ya taimaka wa matan da aka yi masu fade.

Denis Mukwege, wanda likitan haihuwa ne, ya amshi kyautar Sarki Baudouin ta masu kawo cigaba a duniya a birnin Brussels a jiya Talata.

Mukwege ya kafa wani asibiti a birnin Bukavu da ke gabashin Congo don jinyar matan da aka yi masu fyade

Wannan gidauniya mai zaman Kanata ta Sarki Baudouin, wadda ta bayar da kyautar, ta yaba wa asibitin na Mukwege saboda kula da wadanda aka yi masu fyade a likitance da kuma a shawarance don taimaka wa wadanda abin ya rutsa da su su iya komawa hayyacinsu.

Gidauniyar ta ce cikin shekaru 10 da su ka gabata Mukwege da mukarrabansa sun yi jinyar sama da mata 30,000.

Mukwege ya ce an karrama shi da ba shi wannan kyautar kuma ya gode da ya sami damar magana game da bukatar da ke akwai ta mutane su dau matakan agazawa mata a Janhuriyar Demokaradiyya ta Congo.

Kyautar na zuwa ne da tsabar kudi dala dubu 200. Gidauniyar Sarki Baudouin ce ta bullo da kyautar tun sama da shekaru 30 da su ka gabata don saka wa wadanda su ka dukufa wajen inganta zamantakewa a kasashe masu tasowa.