Tun shekarun zamanin mulkin soja ne dai gwamnatin ta kebe wadannan sa’o’i guda uku, inda ake hana zirga zirgar mutane a birni da kewayen Kano domin Jama’a su gudanar da aikin shara da tsaftace muhallin su.
Kamar yadda takardar karar da lauyan Barrister Ibrahim Baba ya gabatarwa kotun ta nuna wadanda ake kara sune gwamnan na Kano da kwamishinan ‘yan sanda na Kano da kwamishinan shari’a kuma Atoni Janar na Kano da kwamishinan Muhalli kana da ma’aikatar muhalli ta Kano.
Ku Duba Wannan Ma Hanyar Da Ganduje Ya Bi Ya Zabo Magajinsa Ta Sabawa Dimokaradiya-'Yan Jami'iyar APC A KanoBarr. Ibrahim Baba wanda ya yi karin haske game da kunshin karar yace hana mutane zirga zirga a cikin wadannan sa’o'i sun tauye hakkin sa a matsayin na dan jihar Kano da sauran mutane mazauna jihar Kano, yana mai cewa matakin ya ci karo da tanade tanaden ‘yancin walwala da kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa ‘yan kasa da kuma daftarin kare hakkin dan adam na nahiyar Afrika.
A cewar Barr Ibrahim Baba, akwai banbanci tsakanin tsaftar muhalli da haramta zirga zirga Jama’a a gari.
Yanzu dai abin jira a gani shine yadda zata kaya a gaban babbar kotun ta Kano.
Saurari cikakkeb rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5