Nutsewar jirgin mai suna Tutor a Tekun Bahar Maliya ya yi kama da mafarin kara tsanani a irin matakan da 'yan Houthis masu samun goyon bayan Iran su ke daukawa na auna jiragen ruwa a muhimmiyar mashigar ruwa a yakin Isra'ila da Hamas a zirin Gaza.
Harin dai na zuwa ne duk da kwashe tsawon watanni da Amurka ta yi ta na jagorantar wata hobbasa ta tsaro a yankin da ya sa sojojin ruwan kasar ke fuskantar yakin ruwa mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu, inda ake kai hare-hare kusan kullum kan jiragen ruwa na kasuwanci da na yaki.
The Liberian-flagged, Greek-owned-and-operated Tutor sank in the Red Sea, the British military’s United Kingdom Maritime Trade Operations center said in a warning to sailors in the region.
Tutor mai dauke da tutar Laberiya, mallakin kasar Girka kuma mai sarrafa kansa ya nutse a cikin tekun Bahar Maliya, in ji cibiyar kula da harkokin kasuwanci ta ruwa ta sojojin Burtaniya a cikin wani gargadi ga ma'aikatan harkokin tekun yankin.
-AP