Wani jirgi mai saukar ungulu da kamfanin mai na NNPCL ya dauki shatarsa a Najeriye ya yi hatsari.
Jirgin ya fada ruwan teku da misalin karfe 11:22 na ranar 24 ga watan Oktoba dauke da mutum 8 a birnin Fatakwal a jihar Rivers.
“Mun kasa samun jirgin mai lamba 5NBQG wanda kamfanin NNPCL ya dauki shata wanda kuma ya taso daga filin jiragen sama na sojin Najeriya a Fatakwal.
"Jirgin mallakin kamfanin East Winds Aviation ne.” Wata sanarwa da NNPCL ya fitar a ranar Alhamis dauke da sa hannun Darektan yada labarai Olufemi Soneye.
A cewar NNPCL, mutum takwas ne a cikin jirgin wadanda suka hada da fasinja 6 da matuka biyu.
“Ya zuwa yanzu an ciro gawarwakin mutum uku” in ji sanarwar.
Jirgin na helikwafta ya fada cikin ruwan Bonny Finima ne da ke hade da Tekun Atilantika kamar yadda hukumomi suka fada.
Bayanai sun yi nuni da cewa ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana can ana gudanar da ayyukan ceto sauran mutanen da ba a gani ba.