A jamhuriyar Nijer wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun hallaka wasu ma’ikatan kamfanin Foraco mai aiyukan gina famfunan karkara, yayinda wasu suka ji rauni a sakamakon harin da suka kai a jiya da daddare a kauyen Toumour a yankin Diffa.
Bayanai daga mazaunan kauyen Toumour, na cewa da misalin karfe 2 na daren jiya Laraba, wayewar yau Alhamis ne wasu ‘yan bindigar da suka shigo gari akan dawakai, inda suka budewa jami’an kamfanin Foraco wuta, wadanda ke yada zango a ma’aikatar magajin gari, akan hanyarsu ta zuwa karkarar Bosso domin aiyukan gina fanfuna.
Magajin garin Toumour Alhaji Mani Orte, yayi ma shashen Huasa na Muryar Amurka bayanin, inda ya tabbatar da faruwar wannan al’amarin. Kauyen Toumour mai yawan al’uma kusan 13,000 nada nisan kimanin kilomita 80, daga gabacin Diffa babban birnin jihar, yayinda ta bangaren kudu garin ke da nisan kilomita 7 da iyaka da jihar Borno a Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5