Motar dake dankare da bama baman ta tarwatsa kanta ne a kan hanyar Maka al-Mukarama dake kusa da majalisar dokoki yayin da jami’an tsaro ke kokarin tare motar domin a binciketa. Nan da nan kungiyar ‘yan bindigar al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.
"Motar taki saurarawa harbi gargadi ta kuma kutsa a guje a cikin tarin jami’an tsaro da suke kula da shingen da dakarun fadar gwamnatin kasar suka kafa, inda bam din ya tashi mu kuma muka ci gaba da zubawa mator harshashai", inji wani jami’in tsaro Aden Mohamed yana fadi bayan harin.
Wakilin Muryar Amurka yace ya ga gawarwaki akalla bakwai kuma yaga mutane da dama sun jikata a lokacin da motocin daukar marasa lafiya ke kwasan su. Asibitoci sun tabbatar da mutauwar mutane uku da suka ji munanar raunuku.
Wakilin Muryar Amurka yace gine gine da dama dake wurin sun lalace wasu ma sun rushe, lamarin da ya tada kura da hayaki da suka turnuke sama.