Wani taron gaggawa da Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta gudanar, ya cimma matsayar cewa, matsalar barkewar cutar Ebola a gabashin kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, ba ta zama bukatar gaggawa da kuma abin damuwa ga fannin kiwon lafiya na duniya ba.
Amma kwamitin kwararru ya yi garagdin cewa rashin isassun kudade, na barazana ga yakin da ake yi da cutar mai saurin kisa.
“Akwai yiwuwar mu ga an dauki matakan dakatar da tafiye-tafiye da harkokin cinikayya, da kuma rufe kan iyakoki, hakan zai matukar shafar tattalin arzikin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congon.” Inji mukaddashin kwamitin gaggawa a hukumar ta WHO, Preben Aavitsland.
Sama da mutum 1,400 suka mutu a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar ta Congo, sannan sama da mutum 2,100 suka harbu da cutar.
Hakan ya sa, a wannan karo na barkewar cutar, ya zamanto mai matukar hadari a yankin arewacin Lardin Kivu da ke fama da tashin-tashina, tun bayan irin wacce aka gani a shekarar 2014 a yankin Yammacin Afirka, wacce ta kashe mutum 11,300.
Facebook Forum