Wani Hakimi Ya Yi Gumurzu Da Masu Kokarin Sace Shi Su 9 Ya Hallaka 2

.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana wasu masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ne suka kutsa cikin gidan wani mai unguwa

Shi dai wannan hakimin kauyen na Mayo Selbe dake karamar hukumar Gashaka a jihar Taraban, Jauro Hammangabdo, ya samu nasara ne akan gungun masu garkuwa da mutanen da suka kawo masa farmaki cikin dare to amma basu taki sa’a ba da nan take ya kashe biyu daga ciki tare da raunata uku daga cikin masu garkuwar.

Shi dai hakimin Hammangabdo, tunkarar maharan yayi lokacin da suka ziyarci gidansa cikin dare, kuma kamar yadda rahotonni suka tabbatar, y’an garkuwar su tara, sun sami nasarar shiga fadar tasa cikin dare kuma nan take suka zarce zuwa makwancinsa, to amma kuma hakimin yayi ta maza tare da yin kukan kura akan wadannan mahara dake kokarin sace shi, kuma kafin kace kwabo ya samu nasara akansu tare da sharba musu takobi-gayawa jini na wuce nan take biyu suka mutu kana sauran suka ranta ya a na kare suka gudu suka bar bindigoginsu.

Ganin wannan na mijin kokari nema yasa mataimakin gwamnan jihar Taraba Haruna Manu ya kai ziyara da jajantawa ga mai martaba Lamido Gashaka, Zubairu Hammangabdo, wanda babban yaya ne ga wannan hakimi inda mataimakin gwamnan ya yaba da wannan kokari na hakimin.

Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin shugaban karamar hukumar ta Gashaka, Mohammed Gayam, yace koda yake hakimin Hammangabdo ya dan samu rauni a hannu da kai, da ta kai an kwantar da shi a wani asibitin sojoji na bataliya ta 20 dake Serti, yanzu yana samun sauki.

Yace, masu garkuwan da aka kashen tuni aka gano su sakamakon faduwar katin shaidan su wato ID card, yace suna cikin masu garkuwa da mutanen da suka addabi yankin,kuma sukan fake ne da sunan ‘yan banga ko ‘yan sintiri.

Shugaban karamar hukumar yace ko a makwannin nan, kusan mutane 17 ne aka yi garkuwa dasu inda aka kashe uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da sun sakamakon rashin biyan kudin fansa daga wadanda suka yi garkuwa dasu.

Shima da yake Karin haske kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Taraban,ASP David Misal ya bukaci jama’a rika bada bayanai na gano mabuyar wadannan bata gari.

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Hakimi Ya Yi Gumurzu Da Masu Satar Mutane 9 Ya Halla 2 Cikin Dare