SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da aka kammala Jana’izar mutane 29 da suka rasu sanadin nutsewar wani kwale kwale a jihar Sakkwato dake Arewa maso yammacin kasar.
Salwantar gomman rayuka na ‘yan Najeriya yanzu ba sabon abu bane sai dai ta fuskar da aka samu salwantar rayukan ne kan nuna alhinin jama'a akan rashin.
Irin wannan sauti ne ke fitowa a wasu gidaje a garin magana dake karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato inda kwale kwalen ya nutse da matasa ya hallaka 29 daga cikin su.
Shugaban karamar hukumar Aliyu Dantanin Shagari yace dama mutanen garin sun saba tsallaka wannan ruwan suna gudanar da al'amurransu na yau da kullum.
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal yace ya kadu matuka da samun labarin wannan ibtila'in.
Wannan dai ba shine karo na farko ko na biyu ba da aka sami asarar rayukan sakamakon hadarin kwale kwale a karamar hukumar Shagari domin ko a farkon watan Yuni na shekarar bara an samu irin haka a garin Ginga inda mutane 13 suka halaka, kuma gwamnatin jihar ta ja kunnen jama'a akan a rika bin ka'idar shiga kwale kwale har tayi alwashin samar da rigunan kariya ga masu shiga ruwa.
Ku Duba Wannan Ma Mutanen Da Suka Tsere A Kwale-kwale Daga ‘Yan Bindiga A Jihar Neja Sun Nutse A TekuMasu lura da al'amurran yau da kullum na ganin cewa dole ne mahukunta su kula da kare rayukan jama'ar su.
Hatsarin kwale kwale dai yayi ta lakume rayukan ‘yan Najeriya a sassan kasar daban daban kamar wanda ya faru a watan Mayu na shekarar bara a garin Warrah na jihar kebbi wanda ya halaka rayuka fiye da dari daya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5