‘Yan sanda a arewa maso yammacin Birnin Muenster da ke Jamus, sun ce wata mota ta yi kan wani cuncurundon jama’a, har ta kai ga wasu sun rasa rayukansu.
Har ila sun ce an samu wadanda suka jikkata.
‘Yan sandan yankin sun aike da sakon Twitter suna cewa “an samu asarar rayuka da kuma wadanda suka jikkata.”
Sun kuma yi gargadi ga jama’a, da su guji yin riga malam masallaci kan dalilin kai wannan lamari, domin a cewar ‘yan sandan yanzu suke kokarin tattara bayanai.
An kuma yi gargadi ga jama’a da su kaucewa ratsawa ta tsakiyar Birnin na Muentser.
Wasu rahotannin sun ce, direban motar ya harbe kansa, amma kuma ‘yan sandan ba su tabbatar da aukuwar hakan ba.
Duk da cewa ‘yan sandan ba su tabbatar da dalilin harin ba, rahotanni sun nuna cewa harin ya yi kama da hare-haren ta’addancin da kasar ta Jamus da Faransa suka sha ganin irinsa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa mutane 30 suka ji rauni.