Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Mutanen Da Suka Mutu a Gaza Ya Kai 17


Wasu Falasdinawa a yankin Zirin Gaza
Wasu Falasdinawa a yankin Zirin Gaza

Ma’aikatar lafiya ta yankin Falasdinu ta bayyana mutuwar wani mutumin Gaza wanda sojojin Isra’ila suka kashe a yayin wata zanga zanga da aka gudanar a makon da ya gabata.

Jami’an kiwon lafiya a ma’aikatar lafiyar ta yankin Falasdinu, sun tabbatar ta kawo jimillar wadanda aka kashe a tarzomar da ta auku a Zirin Gaza zuwa 17.

Ya zuwa karshen makon da ya gabata adadin mutane 15 hukumomin yankin na Falasdinawa suka ce sun mutu.

Ma'aikatar har ila yau ta ce wasu daruruwa mutane kuma sun ji raunuka.

Rundunar Sojin Isra’ila ta bayyana cewa sojojinta sun bude wuta ne akan masu zanga zangar a lokacin da wadansu daga cikin su suka yi kokarin rusa shingen da ke kan iyakar su da Falasdinu.

Ta kuma zargi Falasadinawan da jefa duwatsu da bama-bamai cikin kasarta, tana mai cewa 10 daga cikin wadanda aka kashe ‘yan ta’adda ne wadanda su ka yi kokarin haurawa kan iyakar kasar.

Tashin hankalin da ya auku ranar jumm’a a Zirin Gaza shi ne mafi muni da aka samu kashe-kashe mafi muni a tsakanin Isra’ilawa da Falsadinawa tun wanda aka gani shekarar 2014.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG