Fadar gwamnatin Amurka da ake kira White House ta bayyana cewa tasa takunkunmi ga mutane da kanfanoni 38 na kasar Rasha.
Amurka tace ta dauki wannan matakin ne biyo bayan munanan tabio’in gwamnatin ta Rasha akan harkokin demokaradiyyar kasashen yammacin Turai dama sauran sassan duniya.
An fitar da wannan sanar ce a taron manema labarai da akayi jiya jumaa a fadar ta White House, inda sakatariyar yada labrai fadar Gwamnatin,Sarah Huckerbee Sanders tace amma fa har yanzu Amurka tana so tayi aiki da kasar ta Rasha.
Tace abinda kawai muke fata shine ganin kasar ta Rasha ta canza daukacin tabio’in ta, Sanders taci gaba da cewa zamu ci gaba da tattaunawa domin ganin mun samu kyakkyawar dangantaka nan gaba.
Takunkunmin dai zai shafi fitaccen attjirin nan mai dinbin tasiri a harkokin mulkin kasar,da babban kanfanin sarrafa karafa sai kuma fitattun mutanen da suke na hannun damar shugaba Viladimir Puttin, da wasu kanfanoni 12 da suke mallakar wadannan mutanen ne da kuma wasau manya-manyan jamiaan kasar ta Rasha su 17 da kuma kanfanin sarrafa makamai mallakar gwamnati da wasu bangarorin sa, sai bankin kasar, wadannan sune tankunkumin zai mayar da hankali akansu.
Daukacin wadannan rukunin da wannan takunkunmin zai shafa dai za a dakile harkokin dukkan kaddarorin su dake nan Amurka kana a hana Mutanen Amurka yin harkan kasuwanci dasu
A jiya jumaa da yawan ‘yan majilisar dokokin Amurka dama wasu masana harkokin kasa-da –kasa suke na’am da wannan matakin suna cewa wannan abu ne da ya dace ace anyi tuntuni.
Facebook Forum