‘Yan sanda sun tsare mutumin mai shekaru 62 a cibiyar motsa jikin dake birnin Zhuhai na kudancin China sakamakon take mutanen da yayi a jiya Litinin, a jajibirin babban bikin baje kolin jiragen sama da rundunar sojin kasar ta saba gudanarwa a birnin a kowace shekara.
‘Yan sanda sun bayyana mutumin ne da sunan iyalin daya fito daga ciki na “Fan”, kamar yadda yake a bisa al’adar hukumomin China
An gano Fan a cikin motar dauke da wuka, da raunuka a wuyansa da ake zaton shi ya jiwa kansa, a cewar sanarwar. Baya cikin hayyacinsa kuma yana samun kulawar likitoci.
Fan bai gamsu da yadda aka raba kadarorin kudade a harkar rabuwar aurensa ba, a cewar binciken farko da aka gudanar, inji ‘yan sanda.
Kusan sa’o’i 24 bayan aikata laifin, har yanzu ba’a kai ga tantance yawan mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata ba. daya daga cikin asibitocin dake kula da wadanda al’amarin ya rutsa dasu yace akwai fiye da mutane 20 da suka jikkata, kamar yadda kafafen yada labaran gwamnati suka bada rahoto a jiya Litinin.
Ba’a amsa kiraye-kirayen wayar da wakilan kamfanin dillancin labarai na AP suka yi ba, ko kuma an mika su zuwa wasu asibitocin.
AP