Wani Dan Bindiga Ya Harbe Mutum Hudu A Jihar Oklahoma Da Ke Amurka

Yadda motocin 'yan sanda suka yi cincirundo a kofar asibitin da aka yi harbin a jihar Oklahoma

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa dan bindigar ya harbe kansa bayan da ya kashe mutanen.

‘Yan sanda a jihar Oklahoma da ke tsakiyar kudancin Amurka sun ce mutum hudu sun mutu kana wasu sun jikkata bayan da wani dan bindiga ya bude wuta a wani asibiti.

Wani kakakin ‘yan sandan a daren Laraba ya ce sun tuntubi dan bindigar a cikin asibitin Saint Francis da ke garin Tulsa cikin ‘yan mintina bayan da aka sanar da su halin da ake ciki.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa dan bindigar ya harbe kansa bayan da ya kashe mutanen.

'Yan sanda sun ce dan bindigar ya bude wuta a asibitin ne, bayan da ya dora laifin wani matsanancin ciwo baya da ya same shi bayan wata tiyata da aka masa a asibitin.

Shugaban rundunar ‘yan sanda Tulsa, Wendeall Franklin, ya ce mutumin ya sha kiran asibitin yana musu korafin cewa yana fama da matsanancin ciwon baya tun bayan da aka masa aikin.

Harin wanda ya auku a ranar Laraba, na zuwa ne kasa da makonni biyu, bayan da wani dan bindiga ya kashe yara 19 da malamai biyu a wata makarantar firaimare da ke garin Uvalde a jihar Texas, wadanda aka fara jana’izar wasunsu a jiya Laraba.

A ranar Lahadi shugaban Amurka Joe Biden da mai dakinsa Jill Biden suka kai ziyara garin Uvalde don yin ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu.

Biden ya sha alwashin zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya shawo kan 'yan majalisar dokoki, don a samar da sauye-sauyen a fannin dokokin mallakar bindiga, a wani mataki na kawar da wannan matsala da ta jima tana lakume rayuka.