Wani Dan Bindiga Ya Gamu Da Ajalinsa A Yayin Karbar Kudin Fansa

Gunmen

Tawagar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a jihar Ekiti ta sami nasarar kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a wurin karbar kudin fansa a wani dajin da ke tsakanin iyakar jihohin Ekiti da Kwara.

Rundunar 'yan sandan jihar Ekiti, ta bakin kakakinta Sunday Abutu, ta shaida wa manema labarai a Ado Ekiti cewa hadin gwiwar sojoji da ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro da ‘yan banga sun kashe wanda ake zargin kasurgumin dan bindiga ne a cikin dajin Eruku a jihar Kwara.

Abutu ya ce jami’an tsaron sun yi wa ‘yan fashin kwanton bauna ne a daidai lokacin da aka biya kudin fansa naira miliyan 2 da dubu 100 don kubutar da wasu muitane da suka sace, inda suka bi su bayan sun karbi kudin har kuma suka harbe wanda ake zargin.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ya gabatar da gawar wanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Ado Ekiti a ranar Alhamis kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

Abutu ya bayyana cewa jami'an tsaro sun sami nasarar ceto mutanen biyu da aka biya kudin fansa don ceto su da ransu a yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin kama sauran masu garkuwa da mutanen da suka tsere a yayin artabu da su.

A halin da ake ciki kuma wadanda suka yi garkuwa da daliban rukunin makarantar Gloryland da ke garin Igarra na jihar Edo sun tuntubi iyayen wadanda abin ya shafa suna neman kudin fansa naira miliyan 100.

‘Yan bindigar sun sace daliban ne a ranar Talata a kan titin Igarra-Auchi, kusa da garin Ikpeshi.

Iyayen daliban da aka sace sun nuna damuwar matuka kan lafiyar ‘ya’yansu suna neman a taimaka wajen samun nasarar sako daliban cikin koshin lafiya.

Haka kuma, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Edo, Bello Kongtons, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin sace daliban makarantar Gloryland ba.

Majalisar dokokin jihar Edo ta yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su hada kai don ganin an sako duk wadanda aka yi garkuwa da su.