Wani Binciken Kudade A Nijar Ya Bankado Masu Wawurar Kudin Gwamnati

Bazoum Mohamed

A jamhuriyar Nijar kotun dake kula da yadda aka kashe kudaden gwamnati ta fitar da rahoton binciken da ta gudanar a fannoni da dama na wasu ofisoshin hukuma da kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnatin kasar.

NIAMEY, NIGER - Binciken da yanayin tafiyar da ayyuka a kananan hukumomi har ma da batun kula da kudaden tallafin da jam’iyun siyasa ke karba daga wajen gwamnati, ya ba kotun damar bankado abubuwan asha masu tarin yawa.

Rashin mutunta ka’idar aiki ko yin gaban kai wajen kasafta kudaden hukuma da rashin sanin makamar aiki na daga cikin matsalolin da kotun cour des comptes ta ce ta gano a yayin ayyukan binciken da ta gudanar a ma’aikatu da dama na gwamnati da masu zaman kansu.

Shugaban kotun mai shara’a Narey Oumarou ya ce binciken da suka gudanar a wasu kungiyoyin ayyukan ci gaba ya gano yadda a wasu wuraren aka fake da annobar coronavirus a matsayin wata hanyar cuwa-cuwa a yayin bada kwangila.

A fannin kasafta kudaden gwamanti kotun ta gano hazo tattare da yadda wasu ma’ajin kudaden gwamnati ke gudanar da ayyukansu. Yayinda a wasu ofisoshin ba a ga takardun shaidar kashe kudaden hukuma ba da dai wasu tarin matsalolin da suka shafi ayyukan kula da kudaden kasa.

Mamba a kotun kasafta kudaden hukuma Oumarou Issaka ya zo da misalai na abubuwan ba daidai ba da kotun ta bankado a rahotonta na 2021.

Kundin tsarin mulkin kasa a ayarsa ta 149 ya tilasta wa kotun gabatar da rahotonta ga shugaban kasa da shugaban majalisa da Firai Minista sannan ta sanar da jama’a abubuwan da ta gano bayan gudanar da binciken shekara-shekara haka kuma ya zama wajibi a gareta ta zo da shawarwarin da take ganin zasu taimaka a warware matsalolin da ake fuskanta. Sai dai bayanai na nunin jami’ai na fatali da wadanan shawarwari na gyara kayanka.

Sanar da kotun Cour des Comptes dukiyar da kowanne daga cikin manyan mukarraban gwamnati ya mallaka a kowace shekara wani abu ne da doka ta yi umurni akansa sai dai a cewar alkalan kotun guda ne ke biyayya ga wannan tsari yayinda mafi yawancin masu bin ka’idar kan bada bayanan dukiyoyinsu a makare.

Shugaban kungiyar AEC Moussa Tchangari na daga cikin jami’an farar hular da suka halarci zaman gabatar da rahoton na 2021.

Sabanin yadda aka saba a shekarun baya, a wannan karon kotun ta Cour des Comptes ta bayyana a fili karara sunayen wasu manyan jami’an da suka tafka ta’asa wajen gudanar da aiki donganin abin ya zame wa masu rike da dukiyar kasa abin ishara ta yadda watakila zasu canza hali.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Binciken Kudade A Nijar Ya Bankado Maso Ta’azzara Da Kudin Gwamnati