WASHINGTON DC —
Dakunan karatu na gwamnati, wato bibliotheque ko Library a wasu manyan biranen Jamhuriyar Nijar na fuskantar koma baya, sakamakon raguwar masu amfani da su, lamarin da wasu manazarta ke cewa ya na nuna raguwar tabi’ar karance-karance.
Kazalika, dakunan karatun suna fuskantar matsalar kudi da rashin isassun fasahohin karatu na zamani- ICT Mansour Sani ya ziyarci wani dakin karatu da aka gina sama da shekaru 30 da suka gabata a Maradi domin ganin yadda lamarin yake.
Saurari cikakken shirin cikin sauti: