Benen wanda a halin yanzu ake kan aikinsa ya rikito ne da yammacin ranar Alhamis a kan wasu ‘yan kama wuri zauna da ke fakewa a ciki.
Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce tuni kwamishinan 'yan sandan birnin ya isa wurin da abin ya faru.
A cikin wata sanarwar da ta aikewa Muryar Amurka da dauke da sa hannun kakakin ‘yan sandan birnin Abuja, DSP Josephine Adah, ta ce rundunar ta kuma tura jami'anta don tallafawa jami'an aikin agaji da kuma tabbatar da cikakken tsaro.
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya (FCT-FEMA) ta tabbatar da kwashe mutane da dama daga cikin ginin.
“Ya zuwa yanzu an ceto mutane 19, sannan kuma 1 ya ji rauni,” in ji Nkechi Isa, jami’in hulda da jama’a na hukumar.
Ya ce “an kai wadanda abin ya shafa zuwa asibitocin Wuse, Gwarinpa, Asokoro da kuma Cibiyar Lafiya ta Tarayya.”
Isa ya kara da cewa, wasu kamfanonin gine-gine da manyan kayan aiki suma suna cikin masu aikin ceton.
Kawo yanzu dai ayyukan agaji na ci gaba da gudana yayin da kuma ake jiran irin matakan da mahukunta zasu dauka bayan komai ya lafa da kuma gudanar da bincike.