Fadar White House a jiya Lahadi ta kare ayyana dokar ta baci da shugaba Donald Trump ya yi don ya iya gina Katanga a kan iyakar Amurka da Mexico domin ya hana kwararowar bakin haure duk da ya ce ba dole sai ya yi hakan ba.
Wani mai ba wa shugaba Trump shawara wanda ke da tsattsauran ra'ayi kan batun bakin haure mai suna Stephen Miller ya gaya wa gidan talabijin na Fox News jiya Lahadi cewa Trump, a ta bakinsa, “Na iya kin daukar mataki game da wannan matsalar, to amma bai zabi yin hakan ba."
Miller ya caccaki tsohon Shugaba George W. Bush dan jam’iyyar Republican saboda, abin da ya kira, “cin amanar kasa sosai” na sama da shekaru ashirin da suka wuce, lokacin da ya bari bakin haure suka shigo kasar ninki hudu na masu shigowa yanzu. To amma Miller ya ce, "maganar ita ce: babu yadda za a ce ga kasa gawurtacciya amma kuma ba ta da kan iyaka mai kariya."
Ya ce matakin da Trump ya dauka “na kare kan iyakokinmu ne” sannan ya kira bakin haure "barazana ga kasarmu."