Akalla baki masu kaura daga Honduras 9,000 ne suka tsallaka Guatemala ranar Asabar 16 ga watan Janairu a wani ayari da ya fara tafiya tun ranar Juma’a, su na fatan isa Amurka a kwanakin farko na sabuwar gwamnatin da za a rantsar.
Da farko, ‘yan sandan da ke wuraren bincike da aka ajiye a kan manyan hanyoyi a Honduras da Guatemala sun tambayi bakin takardun shaida amma basu ma yi wani yunkurin dakatar da masu kaurar ba.
Gwamnatin Guatemala ta fitar da wata sanarwa ta na yin kira ga hukumomin Honduras da su dauki matakan magance matsalar kaurar ‘yan kasar da yawa, ta hanyar daukar matakan din-din-din.
Ayarin masu kaurar, da ke tafe da kafa, sun ce zasu yi karfin halin jurewa tafiyar dubban kilomitoci don ratsawa ta Guatemala da Mexico zuwa Amurka, saboda suna gujewa talauci, rashin ayyuka, miyagun kungiyoyin bata gari da masu mu’amala da miyagun kwayoyi, da kuma bala’i a kasarsu.