Lamarin da kuma yasa zaben fidda dan takaran jam'iyar ke lilo tsakanin shugaban dattawan jamiyar ta APC Bola Ahmed Tinubu da kuma mataimakin shugaban Najeriya Yemi Oshibanjo.
Yanzu dai kawuna sun rarrabu tsakanin magoya bayan manyan yan siyasan biyu na jihar lagos.
Kamar yadda wasu magoya bayan su ka sheda wa Muryar Amurka- wasu masu goyon bayan Osinbajo dai na ganin yana da sauran kuruciya don haka zai fi dacewa da zamanin da ake ciki na matasa masu jini a jika, to sai dai masu goyon bayan Tinubu na ganin yafi kwarewa a harkar siyasar Najeriya, kuma yayi mulki a Legas an gani, akwai shi kuma da tafiya da talakawa.
Shi dai Bola Ahmed Tinubu ya kasance tsohon dan siyasa da ya dade yana jan zaren sa tun lokacin siyasar da ta kai ga zaben 12 ga Juni har ya kai ga zama gwamnan Lagos a shekarar 1999.
Shi kuwa Yemi Osibanjo ya kasance tsohon kwamishinan sharia a karkashin gwamnatin Bola Tinubu kuma Tinubu ne ya gabatar dashi a matsayin mataimakin shugaban kasa da ta kai ga kafa gwamnatin Muhammadu Buhari tun daga zaben 2015 zuwa yanzu.
A yayinda shirye shirye yayi nisa domin gudanar da taron kasa da kuma zaben fidda gwani na shugabancin jam'iyar ta APC mai mulki a karshen watan da muke ciki, lokaci ne kawai zai tabbatar da wanda 'ya'yan jami'ar ta APC zasu zaba domin karbar mulki daga hannun shugaban kasa maici a zaben 2023. Idan har yam iyar ta samu nasara kenan a babban zaben na kasa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5