Wadanda Suka Sace Tagwaye A Zamfara Sun Yi Nadama

Wadanda su ke yin garkuwa da mutane a Zamfara

Biyo bayan kame gungun yan fashin nan a Zamfara da suka sace yan biyun nan a kauyen DAURAN dake karamar Hukumar Zurmi, muryar Amurka ta tattauna da daya daga cikin jagororin yan Bindigar.

Daya daga cikin 'yan fashin, Nafiu Usman Wanda Yaro ne dan shekara 28, dan asalin karamar hukumar Zurmi ya ce sun yi Sabo ne da yan bindigar yayin da Suke zuwa sayayya a kauyukansu.

Ya ce ta haka suka Samu sukai Sabo dasu a hankali a hankali har Suke Jan hankalinsu suma Suke zama yan bindigar.

Yace wani Mai suna Yellow shi ya basu shawarar sace yan Matan Ana dab da yin bikinsu, Nafiu yace sun yi amfani da babura shida suka je har gida suka sato Tagwayen.

Nafiu ya zargi yan'uwansa yan bindigar da suka shirya karban kudin fansar da yi masu magudi, inda yace bayan sun karbo Naira miliyan goma sha biyar, sai suka masu karyar cewa Naira Milyan Goma ne, inda suka raba Naira dubu Dari biyar biyar, a hakan ma wasu nasu bai zo hanun su ba.

Daga nan yayi nadamar yadda suka Rungumi wannan sana'ar ta satar mutane.

A nasa bayanin, Kakakin rundunar yansanda Najeriya Moshood jimoh ya ce kimanin manya manyan bindigogi Guda shida, harsasai da takubba suka kama a hanun yan bindigar.

Dukkannin yan bindigar dai zamfarawa ne, Kuma ko a baya Wamban jihar Abdul'Azeez Yari Abubakar Ya koka da Cewar yan bindigar dake aiwatar da kashe kashe dukksnninsu yan jihar ne.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina

Your browser doesn’t support HTML5

Yan fashi a Zamfara sun yi nadama-3:00"