Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Nuwamba 1, 2018: Garkuwa da 'Yan Biyu A Zamfara


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Yau shirin Domin Iyali zai haska fitila kan wadansu batutuwa da suka shafi cin zarafin mata da ya dauki hankalin al'umma kwannan nan da suka hada da labarin ganin 'yammatan Chibok 57 a kasar Kamaru da bisa ga bayani, wadda ta kubuta ta shaidawa jami'an tsaro da dadewa sai dai har yanzu, ba a sami wani bayani daga hukumomi ko na Najeriya ko kuma na kasar Kamaru ba.

Sai kuma labarin sace wadansu 'yan mata uku a jihar Zamfara da suka hada da wadansu 'yan biyu da suke shirin aure.

Shirin ya kuma tabo batun yarinyar nan 'yar shekaru goma sha uku Ochanya Elizabeth Ogbaje wadda ta rasu ranar goma sha takwas ga watan da ya gabata, sakamakon ciwon yoyon fitsari da kuma wadansu matsaloli da tayi fama dasu, biyo bayan cin zarafinta da kawunta dan shekaru hamsin da biyu, malami a makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Benue mai suna Andrew Ogbuja, da dansa Victor suka yi ta yi mata na tsawon shekaru biyar.

A cikin hira da aka yi da ita bayanda wata kungiya mai zaman kanta ta shigar da kara, Ochanya ta bayyana yadda Victor ya rika yi mata fyade, bayan da aka shaidawa kawunta, maimakon ya kare ta, sai shima ya shiga yi mata fyade tare da dan nashi har na tsawon shekaru biyar.

A yau shirin ya tattauna da wata tsohuwar 'yar jarida kuma 'yar fafatuka Ene Ede wadda ta fito daga wannan yankin domin jin ta bakinta kan wannan lamari da ya sa kungiyoyi da dama a jihohi dabam dabam na Najeriya da kuma birnin Tarayya Abuja suka rika zanga zanga suna neman ganin an dauki hukumci tsats-tsaura kan wannan malamin da dansa.

Saurari cikakken shirin.

Sace 'Yan biyu a Zamfara-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:36 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG