A baya, sai da kasar ta shafe makonni uku kafin adadin ya karu daga miliyan 7 zuwa miliyan 8.
Amma a ranar Juma’a, kasar na da adadin wadanda ke dauke da COVID-19 miliyan 9,018, 500, cutar da coronavirus ke haddasawa, yayinda mutum dubu 229,356 suka mutu kamar yadda Johns Hopkins ta wallafa. Jami’an Lafiya sun ayyana karuwar cutar ga sake barkewar cutar tun daga tsakiyar watan Oktoba.
An samu karuwar cutar da kashi 14 cikin dari ne a makonni biyun da suka gabata bisa yadda mutum 800 ke kamuwa da cutar a kullum.
Jami’ar Johns Hopkins ta ce, Jihohin Amurka 47 ne suka samu karuwar cutar a kasar, inda jihohin da dama suka sami sababbin kamuwa a rana guda, ciki har da jihohin Illinois, da Wisconsin da Ohio dake tsakiyar yammacin kasar. Jihohin Texas da California da Florida suma sun shiga wannan tarihi na adadi mafi yawa a rana guda.
Wannan karuwar ta coronavirus a fadin duniya ya sake tilasta shugabannin kasashe su sake daukan matakan kulle domin dakile karuwar yaduwar cutar.
Ministan harkokin wajen Britaniyya Dominic Raab ya fadi a wata hira da Talabijin din BBC a ranar Juma’a cewa ba’a kauda yiwuwar sake daukan matakan kulle kasar shi ba domin hana yaduwar cutar, inda ya kara da cewa matakan cikin gida zasu dauka da sukafi inganci a kowane bangare.
Bayanan na Raab na zuwa ne bayanda shugabannin Faransa da Jamus suka sanar da sake kulle kasashensu a cikin makon.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da sake kulle duk fadin kasar na wata guda da ya fara a Juma’an nan. Macron yace, gidajen cin abinci da wuraren shan barasa da Café Café da wuraren kasuwanci da bana bukatar yau da kullun ba zasu kasance a kulle, yayinda za’a kyale yan kasa su je aiki da sayan kayan masarufi da ganin likita.
Jami’ai a Kasar Faransa sun ce mutane yayin da suke gudun kada kullen ya ritsa dasu a ranar Alhamis sun shiga layi mai tsawo da ya kai kilomita 730 na jerin motoci.
Shugabar kasar Jamus Angela Merkel ta sanar da jerin makamancin matakan a kullen na tsawon wata guda a kasarta wanda zai fara a ranar litinin. Banda gidajen cin abinci da na shan barasa da zasu kasance a rufe, wuraren motsa jiki da wuraren raye raye suma zasu kasance a rufe a cikin dokar ta Merkel, amma mafi yawan wuraren kasuwanci, da kantuna da gidan gyaran gashi zasu kasance a bude.
Makarantu da kasashen biyu zasu kasance a bude a lokacin kullen.
Sanarwar takaita zurga zurga da Macron da Merkel suka bada sanarwa a kasashen biyu yayin da suke ta fama da karuwar sabababbin kamuwa da cutar a kullun.