A jawabin da hukumar ta saba yi, babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus yace a makon da ya gabata an ga karuwar kamuwa da COVID-19 mafi muni tun lokacin barkewar cutar. Galibin kasashen arewacin duniya na gani karuwan kwanciyar mutane a asibiti, da kuma batsewar mutane a sashin kulawan gaggawa a Turai da Amurka.
Tedros ya fada a cikin wannan lokaci cewa shugabanni da dama a duniya suna bada muhimmanci wurin kimanta lamarin da kuma daukar mataki, kamar saka dokar hana zirga zirga da yin aiki da daukar karatu a gida da ma wasu matakan dakile yaduwar cutar.
Tedros yace kasashen da suka yi aiki da shawarwarin masana kimiya sun yi nasarar magance cutar da rage yawan mace mace.
Amma yace kasashen da suka saka siyasa ake kuma rashin mutunta shawarwarin ‘yan kimiya da likitoci, ana yada rudani da yawan kamuwa da cutar da ma yawan mace mace.
Facebook Forum