Wacce Rawa Sabbin ‘Yan Majalisun Dattawan Najeriya Za Su Taka?

Taron 'yan Majalisun Najeriya

Sabbin ‘yan Majalisar Dattawa da za su sha rantsuwar fara aiki cikin ‘yan Majalisa 109 a Majalisa ta 9 tun 1999, na cewa kasancewar su sabbi hakan ba za ta sa su koma tamkar ‘yan kallo a Majalisar ba.

Wasu daga ‘yan Majalisar za sun maye gurbin fitattu da a ka sani a Majalisa ta 8 kamar Uba Sani da ya yi nasara kan Shehu Sani da Mr. Ishaku Cliff da ya kawar da Binta Masi Garba da irin Ibrahim Bomai da ya gefentar da nasarar Muhammad Hassan.

Sabon Sanata Uba Sani ya ce zai yi amfani da kwarewar sa a wasu bangarori don tasiri a Majalisar.

Ita kuma Aisha Binani daga Adamawa da ta taba zama a Majalisar Wakilai, yanzu ta samu zama ‘yar Majalisar Dattawa.

Shugabannin addini da sarakuna na kiran rungumar kaddara ga wadanda ba su yi nasara ba da rike amana ga wadanda su ka yi nasara.

Jam’iyyar APC ke da rinjaye a sabuwar Majalisar inda PDP ke biye da ita da irin hakan ne ma ya kasance a zaben 2015.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Wacce Rawa Sabbin ‘Yan Majalisun Dattawan Najeriya Za Su Taka? - 2'35"