Yayin da hukumar zaben ta ke ci gaba da shirinta na tunkarar babban zaben kasar da za’a gudanar a shekarar 2023.
A jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, mai yawan jama’a kimanin miliyan biyar, hukumar zaben ta ce ya zuwa ranar Jumma’ar da ta gabata mutane dubu dari biyu da arba’in da shida, da dari biyar da shaba’in da bakwai ne (246 578) suka yi rajistar.
To Amma kakakin hukumar zaben a jihar Neja, Alhaji Abubakar Kuta, ya ce sun samu matsalar rashin fitowar jama’a tun farkon fara aikin rajistar.
Ya ce kusan shekara guda ke nan hukumar na gudanar da aikin amma sai yanzu jama’a ke ta yin tururwa fitowar domin rajista.
Ku Duba Wannan Ma INEC Za Ta Rufe Aikin Rijistar Zabe A Ranar 31 Ga Watan YuliWannan matsala ta rashin fitowar jama’a ne yasa kungiyoyi da ‘yan siyasa da sauran shugabannin jama’a suka dukufa wajan fadakarwa akan muhimmancin yi ko sabunta katin zabe.
Ko a karshen makon nan ma wata kungiyar siyasa ta jami’iyyar APC mai goyon bayan Ahmed Bola Tinubu da Muhammad Bago na jihar Neja sun shirya irin wannan taro a Kontagora.
Shugaban taron Alhaji Ibrahim Mamman Abbas ya ce dalilinsu na yin wannan taro shi ne hukumar zabe ta ce an bar yankin arewacin kasar a baya, shi ne ya sa suka tashi tsaye wajen fadakar da jama’a su je su yi rajista.
Ku Duba Wannan Ma Gwamnar Legas Ya Amince Da Wa'adin Kwanaki 4 Domin Samun Katin ZabeA nasa bangaren Abdulhamed El-Wazir Talban Kontagora ya ce ya yaba da aikin hukumar zabe kan yadda ta kara lokaci da kuma zakulo mutane da dama musamman mata da shekarun bai kai ba a wance lokaci domin su yi katin zaben.
Shima Shugaban karamar hukumar Wushishi, Danjumma Suleman Nalango, ya ce sun yi kokari wajan fadakar da jama’a a yankunan karkara.
A yanzu dai akwai ‘yan Najeriya da dama masu cike da fatar ganin hukumar zaben ta kara wani lokacin, domin wata kila ya taimaka wajan bada dama a gyara wasu kura kurai a kan aikin.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5