Vincent Enyeama ya fitar da sanarwar cewa ya fita daga cikin tawagar kungiyar Super Eagles.
Da alamar dai wannan hukuncin da ya yanke na da alaka da abin da ya faru tsakanin ‘dan wasan da kocinsa, wato Sunday Oliseh a wannan makon, bayan da ya isa masaukinsu a kasar Belgium.
An dai bai wa Enyeama izinin zuwa kasar a makare, a dalilin jana’izar mahaifiyarsa da a ka yi a Akwa Ibom. Ya yi kokarin yin bayani a lokacin da suke cin abinci amma Oliseh ya umarce shi da ya zauna ya yi shiru.
Bayan musayar ‘yan kalmomi tsakanin Enyeama da Oliseh, sai Oliseh ya kira dogarawan tsaro domin su fitar da Enyeama.
Duk da cewa hukumar kwallo ta Najeriya NFF ta shiga maganar, har Enyeama ya hakura ya zauna, yanzu kuma ya canza shawara kan bugawa kasarsa wasa.
A safiyar yau Alhamis ne Enyeama ya kafe a shafin Instagram inda ya ke cewa, “Na yi wa kasata yaki har na sama da shekaru 13, na gama aiki na, na rike abin da amana, da kuma raira taken Najeriya da kishi, daga yanzu na ajiye makami na, wanda Allah ne kadai zai iya saka min aikin da na yi har na tsawon shekaru 13. Allah ya albarkaci Najeriya. daga yanzu kuma na bar mukamina na kaftin din tawagar Najeriya, kuma na ajiye matsayina na mai tsaron gidan kungiyar, ba zan sake yin duk wani wasa da ya shafi Najeriya ba. ina son na mika godiya ta ga magoya bayan Najeriya da ke duk fadin duniya. Wannan lokaci ne mai matukar wahala a rayuwata, amma nasan ‘yan Najeriya na tare da ni kuma Allah na tare da ni. Allah ya Albarkaci Najeriya.”