A lokacin da take raban ragunan, sallah Nana Fatima Shettima, uwargidan gwamnan jihar Borno ta kira masu hali musamman masu hannu da shuni da su dinga taimakawa al'ummar da suka samu kansu cikin halin kuncin rayuwa.
Tace ya zama tilas ta rabawa gwaurayen da marayu da suka rasa mazajensu da iyayensu sanadiyar rikicin Boko Haram ragunan sallah domin su yi sallah cikin farin ciki. Saboda haka yakamata mutane su tashi su taimaka.
Nana Fatima tace yanzu haka an bar mata da dama da basu da adadi da suka rasa mazajensu tare da dimbin yara marayu. Ta kira a taimaka musamman lokacin bubukuwan sallah.
Inji wasu da suka samu taimakon sun ce gwauraye sun kai dubu biyar kana marayu sun haura dubu shida. Sun yi mata addu'a tare da godiyar abun da tayi masu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5