Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Sallah Gwamnan Borno da Gwamnatinsa Zasu Koma Bama da Zama


Gwamnan Borno Kashim Shettima zai koma Bama tare da cibiyar gwamnatinsa.
Gwamnan Borno Kashim Shettima zai koma Bama tare da cibiyar gwamnatinsa.

Ganin yadda mutane ke yin dari darin komawa Bama da garuruwan dake kewaye da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun 'yan ta'adan Boko Haram ya sa gwamnan jihar Borno yanke shawarar barin Maiduguri ya zauna a Bama domin ya dinga sa aikin sake gina garuruwan.

A zantawar da yayi da Muryar Amurka gwaman jihar Borno Kashim Shettima ya bayyana irin ayyukan sake gina wasu garuruwa da suka yi, kuma zasu cigaba da yi har duk mutanen dake gudun hijira sun samu sun koma matsuguninsu.

Yace kama daga hanyar da ta nufi Damaturun jihar Yobe sun gina gidage fiye da dari biyu a garin Maitakolori da Kamsukau inda suka ginawa mutanen garin gidajensu da asibitocinsu da masallatansu. Haka ma suka yi a Auno da Mayinok da Mgamdu.

A can garin Benishaikh sun gyara sakatariyarsu da barikoki. Duk abun da ya cancanta a yi, an yi a garuruwan saboda mutane su samu su koma cikinsu da zama.

Gwamna Shettima yace ko ta halin kaka zasu yi kokari su gina garuruwan. Baicin haka wanshekaren sallah zai kwashe nashi-inashi ya tare a Bama tare da gwamnatinsa kuma sai ya ga abun da zai tubewa Buzu nadi. Yace zasu ga yadda za suyi su gina Bama.

Gwamnan yace zai sa ido akan sake gina Bama saboda a ba mutane matsugunin da zasu koma. Yace muddin Shugaba Buhari na kan mulki yayi imanin zai taimaka masu.

Ga firar da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:56 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG