Shugaba Hu Jintao Ya Kammala Ziyarar Aiki Da Ya Kai Amurka

6.25전쟁 정전 60주년을 기념하여 다양한 행사가 평양에서 열리고 있는 가운데,  참전 노병들이 '아리랑' 축제에서 불꽃 놀이를 구경하고 있다.

Shugaban kasar Sin ko China Hu Jinatao ya kammala ziyarar aiki na kwana hudu daya kawo Amurka,yayinda ziyarar ce ya bunkasa dangatakar tattalin arziki tsakanin kasashen

Shugaban kasar Sin ko China Hu Jinatao ya kammala ziyarar aiki na kwana hudu daya kawo Amurka,yayinda ziyarar ce ya bunkasa dangatakar tattalin arziki tsakanin kasashen, duk da kuma matsin lamba kan kiyaye hakkin bil’adama da ya fuskanta.

Jiya jumm’a ce Mr. Hu ya kammala ziyarar aikin tare da yin taro da manyan ‘yan kasuwa a harabar kamfanin kera kayan motoci na China a birnin Chicago dake tsakiya maso yammacin Amurka.

Magajin garin Chicagon Richard Daley,wanda yake kokarin kwadaitawa kamfanonin China su bude masana’antu a birnin,ya yi shugaba Hu Jintao liyafar cin abincin dare na musamman.

Shugaba Hu ya yi kwana biyu a Washington inda aka masa kyakkyawar tariya da bukukuwa daban daban, duk da zanga zanga daya fuskanta daga ‘yan gwagwarmaya da da wakilan majalisar dokokin Amurka kan rashin mutunta hakkin bil’adama da China. Irin wan nan tarba da ya samu wan nan karo, akasin haka aka masa shekaru biyar da suka wuce zamanin mulkin tsohon shugaba George W. Bush.

Duk haka akwai wakilan majalisar dokokin Amurka uku da suka ki halartar liyafar cin abinci da shugaba Obama ya shirya masa a fadar White House.

Wakilan majalisar dokokin Amurka suna kuma fushi da manufofin tattalin arzikin China da suka hada da zargin tana kariya darajar kudadenta,wadda da dama suke ganin shine yake janye ayyuka masu nagarta daga Amurka. Saboda haka ne ma wasu wakilai suka gabatar da kudurin aza kudin fito kan kayayyaki daga China,idan Beijing ta ci gaba da karya darajar kudinta saboda kaya da take sarrafawa su yi arha.

Shugaban Amurka Barack Obama ya gayawa ma’aikatan kamfanin GE a New York ranar jumma’a cewa, tilas ne cinikayya tsakanin China da Amurka ko wani bangare ya amfana.

A ganawarsu shugabannin biyu sun sanya hanu kan yarjejeniyoyin cinikayya da kuma shawarwari kan muhimman batutuwa da suka hada da Koriya Ta Arewa da kuma mutunta hakkin bil’adama.

A taron manema labarai da shugaban Amurka, Mr.Hu ya amince cewa China tana da sauran aiki kan batun kare hakkin bil’adama.