An tashi baram baram a shawarwari tsakanin Iran da manyan kasashen Duniya da aka yi a Turkiyya kan shirin nukiliyar Farisar da ya janyo gardama.
Babbar jakadaiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton, ta bayyana takaicinta kan wargajewar shawarwarin na kwana biyu,amma ta aza laifin kan Iran. Tana mai cewa
“Mun shiga shawarwarin ne da zummar shata hanyoyin samun ci gaba,kuma munyi bakin kokarinmu na ganin hakan ya faru.Ina bakin cikin bayyana cewa hakan bai faru ba”inji Ashton.
Ashton tace abinda ya hana shawarwarin tabuka wani abu shine dagewar Iran na gindiya sharadin cewa kamin a yi a fara shawarwari tilas a janye dukkan takumkumi da Majalisar Dinkin Duniya ta azawa kasar.
Ashton ta jagoranci tawagar kasashen Duniya masu kujeru na din din din a majalisar Dinkin Duniya da Jamus, a shawarwari da Farisa kan shirin Nukiliyarta da janyo gardama.
kasashen Duniya suna zargin Iran tana fakewa da shirin ne ta kera makaman Nukiliya,zarginda Tehran ta musanta.
Taron na Istanbul ya biyo bayan wadda aka yi a Geneva. Malama Ashton tace a taron na Geneva an amince cewa taron na Turkiyya zai maida hankali wajen tantance shawarwari da aka gabatar.
An ayyana taron kwana biyun da zummar daukan matakai da zasu karfafawa duka sassan guiwa,kamar tsarin da zai bukaci Farisa ta bayar da sinadaran Uranium da ta inganta da darajarsu bashi da kwari ainun,san nan a bata mai da cibiyoyin Nukiliyarta suke bukata.
An jarraba irin wadan nan matakai a a bariya dad a bara.