Ana sa ran shugabannin kasashen duniya da shugabannin gwamnatoci da za su gabatar da jawabai a kan batutuwa da dama da suka shafi rayuwar al’umma.
An gudanar da taruka masu muhimmanci kafin muhawarar da shugabannin kasashe za su yi a wannan Talatar, kamar taro kan tabbatar da muradun karni na raya kasashe masu tasowa wanda Khalifa Sanusi Lamido Sanusi ya halarta.
Taron na bana shi ne na cikon 78 kuma an yi masa take “Sake gina amana da habaka hadin kai na duniya.”
Kimanin shugabannin kasashen Afrika 7 ne za su gabatar da jawabinsu ciki har da shugaba Bola Tinubu na Najeriya.
Shi ma shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo a ranar Laraba zai gabatar da nasa jawabi tare da wasu kasashen Afirka.
Babban abin da mutane suke jira su gani shi ne ko shugabannin soji da suka yi juyin mulki a cikin wannan lokaci za su halarci taron ko za su tura wakilai ne ko kuma ba za su halarta ba saboda Majalisar Dinkin Duniya ba ta amince da halaccinsu ba.
Baki da dama daga sassa na duniya ne suka shigo New York, lamarin da ya kawo cunkuson motoci da ma ya shafin aikin zirga-zirgan masu ababen hawa..
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5